30 Nuwamba 2020 - 12:03
OIC : An Zabi Iran A Kwamitin Kare Hakkin Dan Adam

Taron ministocin harkokin waje na kungiyar hadin kan kasashen musulmi na OIC, ya amince da Iran a matsayin mamba a kwamitin dindindin na kare hakkin dan adam na kungiyar ta OIC ko kuma OCI cewa da (CPIDH).

ABNA24 : An zabi Jamhuriyar musulinci ta Iran ne a kwamitin yayin taron ministocin harkokin wajen kasashen karo na 47 da ya gudana a Yamai babban birnin Jamhuriyar Nijar a ranakun 27 zuwa 28 na watan nan da muke ciki.

Daga cikin kasashe 18 a yankin Asiya, an kuma zabi kasashen Turkiyya da kuma Afganistan a wa’adin wakilcin na tsawon shekaru hudu daga shekara (2021 mai shirin kamawa zuwa 2024).

Baya ga hakan daga bangaren kasashen Larabawa da kuma Afrika an zabi wakilai uku-uku, da suka hada da Saudiyya Masar da kuma Marocco daga kasashen Larabawa, sai kuma Jamhuriyar Benin, tarayyar Najeriya da Nijar daga gungun kasashen Afrika masu wakilci a kwamitin na kare hakkin dan adam na kungiyar hadin kan kasashen musulmi cewa da OIC.

Yaunin da ya rataya a kwamitin, dake da cibiya a birnn Djeddah na kasar Saudiyya, shi ne tabbatar da kare hakkin dan adam, musamman mata da yara, da hakkin samar masu da ilimi, da ci gaba mai daurewa, da yaki da kyammar musulmi da kuma kare musulmi raunana a cikin kasashen da ba na musulmi ba.

342/